Ad Code

Responsive Advertisement

Matashin attajiri ya talauce bayan shirya biki na kece raini, an bar shi da tarin basussuka

 



Wani matashi ɗan Najeriya ya bayyana wani babban kuskure da ya tafka a rayuwar sa.

Matashin wanda magidanci ne wanda yace yana samun miliyoyin kuɗi a wata, ya bayyana cewa yayi kuskuren ɗaukar kuɗin kasuwancin sa domin yin biki na kece raini.

A cewar sa, kasuwancin sa na ta haɓaka, wanda har ya sanya an kai matakin da abokan sa suka zuba kuɗin su a ciki. 

Yatafka aikin danasani

Sai dai abin takaici, bayan sun zuba kuɗaɗen su, sai kasuwancin ya fara ja da baya sannan gashi ya sanya ranar auren sa.

A maimakon ya biya mutanen dake bin sa bashi kuɗaɗen su, sai ya haƙiƙance cewa lallai sai ya shirya biki na kece raini, inda yake tunanin cewa zai mayar da kuɗin sa bayan an gama biki.

Sai dai hakan bai faru ba domin tun daga nan duniya tayi masa atishawar tsaki, inda ya talauce ga kuma ɗumbin basussukan da aka biyo shi.


Post a Comment

0 Comments

Close Menu