Rundunar ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce ta gayyaci mutane takwas masu hidima a gidan shahararren mawaƙin nan Davido, domin gudanar da bincike game da rasuwar ɗan mawaƙin, Rundunar ƴan sanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce ta gayyaci mutane takwas masu hidima a gidan shahararren mawaƙin nan Davido, domin gudanar da bincike game da rasuwar ɗan mawaƙin, mai shekara uku.
Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar wa BBC cewar yanzu haka an ajiye gawar yaron a ɗakin adana gawa.
Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da daddare, kuma ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda.
Kakakin ƴan sandan ya kuma ce sun tattauna da iyayen yaron, yayin da suke ci gaba da bincike. shekara uku.
Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar wa BBC cewar yanzu haka an ajiye gawar yaron a ɗakin adana gawa.
Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da daddare, kuma ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda.
Kakakin ƴan sandan ya kuma ce sun tattauna da iyayen yaron, yayin da suke ci gaba da bincike.






0 Comments