Yadda Maza, Mata Da Kananan Yara Ke Tsallake Rafi Domin Tsira Daga Harin 'Yan Bindiga A Jihar Neja saboda yan ta'adda
Yadda maza da mata dama ƙananan yara, ke tsallaka rafuka da koramu kenan domin tsira da rayukan su, a ƙauyukan Ragada, Mazame da sauran ƙauyukan dake yankin. Sakamakon hare haren da 'yan bindigar ke kai masu tare da bin su gida gida suna dafe su kamar fari.
Na samu zantawa da wasu daga cikin al'ummar yankin, cikin harda Dagacin Mazame, waɗanda suka shaida mani cewar halin da suke ciki a yanzu, ya munana. Domin kusan ɗaukacin al'ummar yankin a daji suke kwana, cikin ruwa da ɗari. Yayin da wasun su suka gudo suka bar ƙauyukan zuwa cikin garin Gulbin Boka.
Ya Allah ka kawo wa waɗannan bayi naka ɗauki, da ma sauran al'ummar dake cikin mawuyacin hali.
Daga kadunasport99






0 Comments